Tambayoyi da amsarsu tare da Mallam Ibrahim Zakzaky na goma sha hudu

In mutum ya tsinci takarda da ayar Kur'ani ya zai yi?
TAMBAYA: Ina so Malam ya yi mani bayanin yadda ake yin taimama a Jafariyya da kuma niyya.
Daga Habibu Zailani Kurmin Darazo Jihar Bauci.
SHAIKH ZAKZAKY: To wannan yana da kyau ya zama ya karanta ne a cikin Risala amaliyya, domin ita taimama tana da wadansu abubuwa da suka shafe ta wadanda suka shafi ba kawai yadda ake yin ta ba, har da dalilan da ke sa a yi ta. To, kuma a takaice dai, ana bugun kasa ne da ma'anar bugu, a shafi goshi da gira har ya zuwa doron hanci da wani abu na kunci da hannuwa biyu, sannan sai a shafi bayan dama da cikin hagu. Sannan a shafi bayan hagu da cikin dama, kowanne daga gaba zuwa karshen yatsu. Sai dai na fi son ya karanta don akwai wadansu abubuwa baya ga 'kaifiyya', ba kawai yadda ake yin ne shi kenan ba.
TAMBAYA: Ni ina kiran Wana da Yaya kamar yadda mahaifiyata ta koya mani, amma ni kuma 'ya'yana suna kiran Yayyensu da sunayensu. Ko akwai laifi?
Daga Abdullahi Garba gama Kankara
SHAIKH ZAKZAKY: To al'adar mutane ne, kuma yana dai da kyau abubuwa irin na ladabi a ce ana koya wa yara irin wannan. Ba ma kawai babu laifi ga yi bane, muna iya cewa ma yana dai da kyau a koyar da mutane abubuwa irin na ladabi. Kamar yadda yake ce wa wansa Yaya, to ya koyawa 'ya'yansa na kasa ya rinka kiran na gaba da Yaya, shi kuma Baba a ce masa Baba ko Abba ko abin da ya yi kama da haka nan. Ita kuma mahaifiya a kira ta Umma ko Mama ko abin da ya yi kama da haka nan, a daina kiran su da sunayensu, tunda ana ganin wannan ba ladabi bane.
TAMBAYA: Na kasance bayan kabbarar harama da kuma sujuda ina yin wasu addu'o'i. Ko ya dace?
Daga Abdullahi Garba gama Kankara.
SHAIKH ZAKZAKY: In ma'asurai ne, domin akwai addu'o'i ma'asurai wadanda ake yi bayan kabbarori din, to babu laifi. Amma in ba ma'asurai bane, to sai mu ce abin da ya fi kawai kada ya yi. Kada ya kirkiro wata addu'a da shi ne yake yi don kashin kansa. Amma in ma'asurai ne wanda aka samu, wato an ruwaito kenan, bayan kabbarar harama wanda akan yi har guda bakwai - bayan ukun farko akwai abin da ake fada, bayan biyu akwai da kuma bayan wasu biyu din kuma da wadansu addu'o'in ma'asurai - babu laifi.
TAMBAYA: Ya hukuncin shan Maltina yake a Musulunci?
Daga Aminu Haruna Kofar Ruwa Kano.
SHAIKH ZAKZAKY: Ya halatta tunda dai ba giya bace. Giyar da ke bugarwa ita ce ta haramta. Ana cewa duk abin da mai yawansa zai bugar, to kadan din sa ya haramta. Amma ita Malt, wanda yakan zo da sunannaki daban-daban a wajen masu saidawa, abin sha ne da ake debowa daga hatsi, kamar alkama ko shinkafa. Kuma shi ba giya bane wanda ake ce wa Beer, wanda ake debowa daga hatsi din. Saboda haka shi ya halatta a sha. Illa iyaka mu dai mukan kyamaci sayen wadannan, duk da dai halas ne. Mukan kyamaci sayen irin wadannan mu sha don ganin cewa wuraren da suke yin su, a nan kuma har wala yau ake yin giya, kamar kuma muna taimaka ma masu yin giya da dan jari wajen ci gaba da 'Business' din su. Amma da za a sami wasu wadanda suke tatso abin sha na halas daga hatsi, wanda shi kuma khasatan na halas din suke yi, to da zai zama ba komai.
TAMBAYA: Menene hukuncin wanda ya ce Manzo kaza, alhali Imam Ali ne ya ce ko wani daga cikin Imamai?
Daga Muhammad Mujtaba Kofar Durbi Katsina.
SHAIKH ZAKZAKY: To idan kuskure ne, tunda duk abin da aka ruwaito daga wajen A'imma zantuka ne da su ma suka samo daga, ko dai kalmomin na Manzon Allah ne ko kuma ilimin sun same shi daga wajen Manzon Allah ne, za mu iya cewa babu laifi, amma in da gangan ne, to sai mu ce ya yi laifi, ko dayake bai shiga ma'anar kirkira ma Manzon Allah karya ba. Abin da ake ce ma kirkira ma Manzon Allah karya, shi ne ka san Manzon Allah bai fadi abu ba, domin ka biya wata bukatarka ka ce ya fada, to wannan shi ne za a ce ka kirkiri karya. Amma ala ayyi halin dai ban ce ana iya ce ma abin da Imam ya fada Manzon Allah ya fada ba, sai dai idan ya zo dama da sigar cewa Manzon Allah ya fada, su kuma an ruwaito daga gare su. In kuma ya tsaya a wajen maganarsu, ana iya kiran shi ma'asuri ko hadisi ko da ba a fadi takamaimen wa ya fada ba.
TAMBAYA: Idan mutum ya tsinci takarda mai dauke da rubutun Kur'ani, zai iya yaga ta ta yadda ba za a iya gane ko menene ba?
Daga Muhammad Mujtaba Kofar Durbi Katsina.
SHAIKH ZAKZAKY: Yana iya batar da rubutun dai ta hanyar da bai zama wulakanci ga rubutun Alkur'anin ba, kamar wankewa masalan in zai wanku, ko kuma a zuba masa wani abin da ba najasa ba, wani 'Chemical' wanda zai iya batar da rubutun ko wani abu mai kama da haka nan. Amma dai ala ayyi halin duk abin da zai yi, in dai a fahimtar mutane bai zama wulakanci a gare shi ba, to ba komai. Kuma in ana ganin konawa a matsayin wulakanci, ba za a kona ba. Sai dai yanzu kamar akwai wani irin abin da yake yanka takarda wanda in an sa yakan maishe shi gari, to kuma ko da gari aka maishe shi tunda yana da alfarmar ya taba daukar Alkur'ani, za a girmama shi ba za a zubar da shi a ko'ina ba, sai a kiyaye, a yi amfani da shi ta wata hanya ta yadda dai, ala ayyai halin kar ya zama za a iya cewa an wulakanta shi.
TAMBAYA: Ni mutum ne mai yawan rihi sai dai ba kowane lokaci ba, amma fakam da yawa tsakanin alwala da sallah rihi kan rinka zuwa mani. To yaya zan gyara sallata?
SHAIKH ZAKZAKY: Sai mu ce, to lallai hukuncinsa hukuncin mabduni ne. Mabduni kuma shi ne wanda rihi ke yawan fita masa. To kamar yadda ya nuna cewa a wani lokaci ba ya zuwa, saboda haka in ya lura da wadansu lokuta da yakan sami hutu daga wannan, to wadannan lokutan ya kamata ya rinka yin sallah. Sai dai lallai ba zai saurara har lokaci ya fice ba, idan ya ga lokaci yana kokarin ya wuce, to sai ya yi salla da hukuncin Mabduni. Wato in har ya iya alwala guda daya, to sai ya yi sallarsa har ya kammala tare da kuma rihin na fita masa din.
TAMBAYA: Nine ina azumi, da safe sai na ji wani abu kamar tuke ya zo mani, sai na ji wani abu a bakina, ni kuma sai na mayar da shi cikin cikina. To a nan Malam yaya hukuncin azumina?
SHAIKH ZAKZAKY: To shi a nan ya nuna yana da shakku tunda ya ji kama ne, saboda haka hukuncin mai shakku shi ne kawai ya dauka ba haka nan din bane. Amma idan abin da ake ce ma kurs, wato magwas, ko dan karamin amai da yakan fito, in ya fito a falalin bakin mutum, to lallai abin da ake so shi ne ya zubar da shi. Saboda haka tunda ya yi shakku sai mu koma ga mai yakini mu ce ba komai gare shi kawai
TAMBAYA: Akramakallahu nine tafiya ta kama ni cikin watana azumi daga garin da na kwana 10 zuwa garina. A ranar da zan bar garin da na kwana 10 sai barci ya kwashe ni da safe har na yi mafarki, to kuma sai na bar garin kafin zawwali. To a nan zan rama azumin wannan ranar ne duk da na bar garin kafin zawwal ?
SHAIKH ZAKZAKY: To na farko, dangane da mafarkinsa, kodayake a nan bai shafi tafiyarsa ba, tunda yake ma babu azumi a kansa, saboda ya taso tafiyar. Don mun kaddara cewa daga inda ya kwana 10 din zuwa garin nasa, tafiyar ta kai 'masafa' na kasaru. Saboda haka zai kasance kenan tunda ya taso kafin zawwal ne babu azumi a kansa. Saboda haka ka ga wato kenan batun janaba da ta same shi ba ta da wani dangantaka da wannan. Kuma ko da yana zaune a garin da yake ne, sai ya zamana ya yi janaba da rana a sakamakon ya yi barci, shi ma in ya farka wanka kawai zai yi ba abin da ya shafi azuminsa. Wanda ainihin janabarsa takan karya masa azumi, shi ne wanda ya wayi gari da janaba din da mantuwa ko kuma ya san da janabar, amma kafin ya yi wanka yana sa tsammanin zai tashi sai kuma ya zama ya tashi alfijir ya riga ya keto, to shi ne ramuwa ke hawansa in yana zaune ne.
TAMBAYA: Allah gafarta Malam mu ma'aikatan Almizan ne, muna baro garuruwanmu, Zariya, Bauchi ko Kano don zuwa Kaduna duk ranar Alhamis don yin aikin ALMIZAN, wata rana muna komawa a ranar, wata rana kuma sai mun kwana. Shin za mu yi kasaru kuma da daina azumi kenan, ko kuwa za mu cika sallarmu mu kuma yi azuminmu?
Daga Sabi'u Abdullahi Kano
SHAIKH ZAKZAKY: To, tunda tafiyar ta kai masafa, saboda haka lallai kasaru da daina azumin ya hau kansu. Amma da sharadin suna baro garuruwan nasu kafin zawwal ne. In mutum ya baro bayan zawwal, to shi kenan zai cika azumi, amma kuma zai yi kasaru. In suka zo bayan zawwal, to azuminsu zai zauna, amma in suka iso za su kwana din nan ka ga za su yi kasarun isha'insu, in za su koma kuma ka ga dole sai su aje azuminsu, tunda da ma in suna Kaduna dole za su sha azuminsu tunda ba suna garinsu bane sun zo aiki ne su koma gida.
.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved